IQNA

21:39 - March 06, 2021
Lambar Labari: 3485719
Tehran (IQNA) Jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika ya bayar da kyauta ta musamman ga kwamandan dakarun sa kai na al’ummar Iraki.

Babban jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Francis yana ci gaba da gudanar ziyarar aiki a kasar Iraki, inda ya bayar da kyauta ta musamman ga Rayyan Kildani, daya daga cikin kwamandan dakarun sa kai na al’ummar kasar Iraki Hashd Alshaabi, wanda kuma shi mabiyin addinin kirista ne.

Paparoma ya bayar da kyautar tasbaharsa wadda yake yin amfani da ita, ga wannan kwamandan na dakarun sa kai na al’ummar Iraki Hashd Alshaabi, a matsayin girmama wa ga dukkanin dakarun da kuma ayyukan da suke gudanarwa na kare kasarsu da al’ummarsu daga ayyukan ‘yan ta’adda.

A yayin mika wannan kyauta da Paparoma ya yi wa wannan kwamnada na Hshd Al-shaabi, babban kwamnadan dakarun na kasa baki daya Faleh Fayyad da kuma wasu daga cikin manyan kwamandojin rundunar duk suna a wurin.

Tun a jiya ne dai Paparoma ya fara gudanar da ziyar tasa a kasar Iraki, inda ya gana da shugaban kasar ta Iraki Barham Saleh, da Firayi minista Mustafa Alkazemi gami da shugaban majalisar dokokin Muhammad Halbusi, da kuma wasu jagororin mabiya addinin kirista a Bagadaza.

Bayan nan a yau ya wuce zuwa birnin Najaf, inda ya gana da bababn malmin addini na kasar ta Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani, tare da duba wasu daga cikin wuraren tarihi da suke birnin.

3957727

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: