A jiya Laraba ne dai Samia Suluhu Hassan wacce take rike da mukamin mataimakin shugaban kasar ta Tanzania, ta sanar da rasuwar shugaban kasar John Magafuli, sanadiyyar bugun zuciya.
Tsarin mulkin kasar ta Tanzania ya yi tanadin cewa wanda yake kan mukamin mataimakin shugaban kasar ne zai karasa wa’adi na biyu na mulkin Magufuli da ya riga mu gidan gaskiya, da zai kare zuwa shekara ta 2025.
Idan aka ranstar da ita sai sa ta zama mace ta farko wacce za ta rike mukamin shugaban kasa a cikin yankin gabashin Afrika.
Ita dai Suluhu haihaffiyar yankin Zanzibar ce kuma musulma wadda ta taka rawa a bangaroririn siyasa a kasar.