IQNA

Kungiyoyin Musulmin Amurka Sun Yi Allawadai Da Harin Ta’addanci A Jihar Colorado

22:29 - March 27, 2021
Lambar Labari: 3485766
Tehran (IQNA) kungiyoyin musulmi a kasar Amurka sun nuna alhini kan kisan da aka yi a jihar Colorado.

Shafin yada labarai na religious news ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da suka fitar, cibiyoyin musulmi a jihar Colorado ta kasar Amurka sun yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai a jihar.

A cikin bayanin da cibiyar musulmi da ke jihar Colorado ta fitar, ta bayyana harin da aka kai da cewa hari ne na ta’addanci, kuma musulmi suna yin Allawadai da duk wani ta’addanci da ke cutar da farren hula.

Baya ga haka kuma cibiyar ta bayyana cewa, tana taya iyalan wadanda suka rasa ruyukansu a wannan hari alhinin abin da ya faru, tare da shan alwashin bayar da taimako na tallafawa masu bukatar taimako daga cikinsu.

Haka nan sau ran cibiyoyin musulmi daban-daban a jihohin kasar Amurka duk sun fitar da bayanai na yin tir da wannan hari, tare da bayyana shi da cewa ya sabawa ‘yan adamtaka.

Harin da wani dan ta’adda ya kai a jihar ta Colorado ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 da suka hada har da wani dan sanda, kamar yadda wasu da dama suka jikkata.

 

3961124

 

captcha