Shafin yada labarai na jaridar Egypt Today ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin al’adu da tarihi ta kasar Masar ta sanar da saka tulluwar masallacin Qaitabai a cikin wuraren tarihi na kasar.
Wannan masallaci tarihinsa na komawa zuwa ga lokacin mulkin sarakunan Qaitabai a kasar Masar, a kan haka aka saka shi cikin muhimman wurare na tarihi.
An gina wannan wuri ne a cikin shekara ta 866 zuwa 899 hijira kamariyya, sannan kuma an saka wasu duwatsu biyu a wurin wadanda wani mutum ya zo da su daga Hijaz, kuma ake danganta su da manzon Allah (SAW) insda sarki Qaitabai ya sayi duwatsun biyu kuma ya bayar da umarni aka saka su a wannan masallaci.
Amma bayan da sarakunan daular Usmaniya suka mamaye Masar, sai suka dauke wadannan duwatsu suka tafi da su zuwa Istanbul, inda aka saka sua masallacin Sultan Ahmad, amma daga bisani wani daga cikin sarakunan daular Usmaniya ya bayar da umarni aka mayar da su zuwa Hijaz a wurinsu an asali.