IQNA

Manhajar Ziyarar Haramomin Makka Da Madina Da Masallacin Quds Ta Yanar Gizo A Watan Ramadan

17:20 - April 05, 2021
Lambar Labari: 3485784
Tehran (IQNA) an samar da wata manhaja ta ziyarar haramin Makka da Madina da masallacin Quds a yanar gizo a cikin watan Ramadan.

Shafin yada labarai na alarabi ya bayar da rahoton cewa, an samar da wata manhaja ta ziyarar haramin Makka da Madina da masallacin Quds a yanar gizo a cikin watan Ramadan mai alfarma.

An samar da wannan tsarin ne domin masu amfani da kafofin sadarwa na yanar gizo su yi amfani da shi kai tsaye idan suna bukatar duba wuraren ziyara a cikin watan Ramadan.

Daga wuraren da manhajar ta kunsa akwai masallacin haramin Makka mai alfarma, wanda ake nuna cikinsa kai tsaye, da kuma sauran bangarorinsa da kusurwoyinsa, haka nan kuma da wajen masallacin harami.

Baya ga haka kuma shirin ya hada da masallacin manzon Allah (SAW) da ke Madina, wanda shi ma ana nuna shi kamar yadda ake nuna masallacin haramin Makka kai tsaye.

Sannan kuma wannan manhaja ta kunshi masallacin quds mai alfarma, wanda shi ma za a iya ganin dukkanin bangarorinsa, da suka hada da babu rahma, da kuam masjid kibla.

Bayanin ya kara da cewa,a kwai sauran wurare guda 14 na ziyara a cikin Makka da Madina da kuma birnin Quds wadanda duk za a iya ganinsu kai tsaye ta hanyar wannan manhaja.

3962432

 

 

 

 

captcha