IQNA

Cibiyar Fikihun Musulunci Ta Duniya:

Allurar Rigakafin Cutar Corona Ba Ta Karya Azumi

23:51 - April 18, 2021
Lambar Labari: 3485822
Tehran (IQNA) cibiyar fikihun muslunci ta duniya ta bayar da fatawar cewa, allurar rigakafin cutar corona ba ta karya azumi.

Shafin yada labarai na Almadina ya bayar da rahoton cewa, cibiyar fikihun muslunci ta duniya ta bayar da fatawar cewa, allurar rigakafin cutar corona da aka yi wa mutum ta karkashin fatarsa ko a cinya ba ta karya azumi.

Kafin wannan lokacin ma cibiyar Azhar ta kasar Masar ta bayar da fatawar cewa, yin allurar rigakafin corona a cikin watan ramadan, ba ya daga cikin abubuwan ad suke karya azumi.

Bayanin na Azahar ya ce, allurar rigakafin cutar corona kamfanonin magunguna na duniya ne suke samar da ita, kuma ana yi ma mutum ita ne ga cinyar hannu, saboda haka wannan ba abinci ba ne ko abin sha.

 

3965539

 

 

captcha