IQNA

An Bude Gasar Kur’ani Ta Sheikhul Qurra Karo Na Biyar A Kasar Mauritaniya

22:39 - April 19, 2021
Lambar Labari: 3485826
Tehran (IQNA) an bude gasar kur’ani mai tsarki mai lakabin Sheikhul Qurra a kasar mauritaniya da ake gudanarwa a cikin watan Ramadan.

Jaridar al-akhabr ta kasar Mauritania ta bayar da rahoton cewa, a jiya ne aka bude gasar kur’ani mai tsarki mai lakabin Sheikhul Qurra a birnin Nuwakshot, wanda ta kunshi bangarorin hardar kur’ani, da kuma tilawa gami da tawidi ko kuma sanin hukunce-hukuncen kira’a.

Makaranta da mahardata kur’ani ‘yan 421 ne daga ciki da wajen kasar mauritaniya suka shiga wannan gasa, inda a halin yanzu ana a matakin farko ne, wanda kuma zai ci gaba daga nan zuwa kwana biyar.

Ana kiran wannan gasa ne da gasar sheikhul Qurra, domin tunawa da babban malamin kur’ani na kasar Murtaniya, sheikhul Qurra Sidi Abdullah Bin Abubakar Al-tanwajiwi.

Idan aka shiga mataki na karshe na gasar, mutane 30 ne kawai za su yi saura a cikinta, inda daga karshe za a zabi mutane 3 wadanda suka fi samun maki, domin zuwa matsayi na daya, da na biyu da kuma na uku.

Bayan kammala gasar za a bayar da kyaututtuka na musamman ga dukkanin wadanda suka fi nuna kwazo.

3965527

 

 

captcha