Tashar Sky News Arabic ta bayar da rahoton cewa, daruruwan kungiyoyin jin kai a kasar Aljeriya suna gudanar da ayyukan taimakon marassa karfi, tare da tallafa musu a cikin watan Ramadan.
Rahoton ya ce, wadannan kungiyoyi akasarinsu kungiyoyi ne na matasa, wadanda suna gudanar da irin wadannan ayyuka a sauran lokuta na shekara, amma suna rubanya ayyukan nasu a cikin watan Ramadan.
Daga cikin ayyukan nasu hard a shirya buda baki tare da gayyatar mutane musamman marassa galihu domin su ci abincin da aka tanada, amma a wannan karon saboda kaucewa yaduwar cutar corona, suna gudanar da ayyukan nasu ne ta hanyar tanadar abinci, da kuma rarraba shi ma mutane gida-gida.
Haka nan kuam sukan raba abincin ga mutane masu wucewa a kan tituna, musamman wanda suka fahimci yana cikin bukata.
Wadannan matasa dai suna gudanar da wannan aikin ne ta hanyar tattara abin da suke samu a wuraren ayyukansu, tare da yin sadaukarwa da shi ga mabukata.