IQNA

A Karon Farko An Girke ‘Yan Sanda Mata A Cikin Masallacin Haramin Makka Mai Alfarma

18:36 - April 20, 2021
Lambar Labari: 3485830
Tehran (IQNA) a karon farko an girke ‘yan sanda mata a cikin masallacin Makka mai alffarma.

Shafin yada labarai na yanar gizo na jaridar Albayan ya bayar da rahoton cewa, a karon farko an girke ‘yan sanda mata a cikin masallacin Makka mai alffarma, da nufin kula da harkokin tsaro a daidai lokacin da masu ayyukan ziyarar umara ke gudanar da harkokinsu.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wanann lamari ya fusakaci martani daga mutane masu bin shafukan yanar gizo, yayin da wasu suke ganin hakan ya dace, domin kuwa zai bayar da dama wajen gudanar da ayyukan tsaro a bangaren da ya shafi mata masu ziyara, wasu kuma suna ganin hakan bai dace ba.

Wannan dai duk yana daga cikin siyasar Muhammad Bin Salman, na bayar ad dama ga mata a dama da su a cikin dukkanin harkokin kasar, sabanin yadda aka mayar da su saniyar ware.

استقرار نیروهای امنیتی زن برای نخستین‌بار در حرم مکی

Yanzu haka dai Bin Salman ya soke dokar da ta haramta wa mata tuki wadda malaman kasar suka amince da ita, ya kuma ba mata damar shiga dukkanin harkokin wasanni da motsa jiki da halartar wurare kallon kwallo da sauran wuraren taruka.

Haka nan kuam yana da niyyar kafa dokar da za ta bai wa mata damar yin aiki ba tare da izini ko amincewar iyayensu ko mazajensu ba, kamar yadda kuma dokar za ta ba su damar yin tafiye-tafiye zuwa duk inda suke so ba tare da muharrami ba, abin da wasu daga cikin malaman kasar suke ganin ya saba wa shari’a, kuma suke da sabani da Bin Salman a kan wannan batu.

 

3965898

 

Abubuwan Da Ya Shafa: karon farko an girke
captcha