IQNA

An Girmama Wadanda Suka Nuna Kwazo A Gasar Kur'ani Ta Duniya A Dubai

23:48 - April 25, 2021
Lambar Labari: 3485844
Tehran (IQNA) an girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar kur'ani ta duniya da aka gudanar a birnin Dubai.

Jaridar Emarat ta bayar da rahoton cewa, an girmama wadanda suka nuna kwazo a gasar kur'ani ta duniya da aka gudanar a birnin Dubai.na kasar hadaddiyar daular larabawa.

An bayar da kyautuka na musamamn ga wadanda suka zo na daya da na biyu da kuma na uku a bangaren hardar kur'ani.

Wanda ya zo na daya a gasar dai shi ne Muhammad Abu Qasim daga kasar Syria, sai kuma sai kuma Abdulganiy Yahya daga kasar Amurka, sai kuma na uku shi ne Muzammil Muhammad daga kasar Sudan.

Sannan kuma an bayar da kyautuka ga wadanda suka zo na hudu har zuwa na goma, da suka fito daga kasashen hadaddiyar daular larabawa, Senegal, Somalia, Bangaladeh, Masar, Nijar da kuma Chadi.

Wannan dai shi ne karo na ashirin da hudu da ake gudanar da wannan gasa a kowace shekara a birnin Dubai, inda take samun halartar makaranta da mahardata kur'ani daga kasashen duniya, inda baya ga kyatuka na musamman da ake bayarwa ga wadanda suka zo na daya har zuwa na goma, ana bayar da kyautuka kuma ga dukkanin wadanda suka halarci gasar.

 

3966922

 

 

captcha