IQNA

An Dakatar Da Wasa A Gasar Premier Domin Dan Wasa Musulmi Ya Yi Buda Baki

23:48 - April 27, 2021
Lambar Labari: 3485853
Tehran (IQNA) an dakatar da wasan kwallon kafa da aka buga a jiya tsakanin Leicester City da kuma Crystal Palace a Buratniya domin dan wasa musulmi ya samu damar yin buda baki.

Alkalin wasa ya dakatar da wasan kwallon kafa da aka buga a jiya tsakanin Leicester City da kuma Crystal Palace a kasar Buratniya domin dan wasa musulmi ya samu damar yin buda baki.

A wasannin Premier League da ake bugawa a kasar Burtaniya, an dakatar da wasan da aka buga a jiya tsakanin Leicester City da kuma Crystal Palace a mintuna na 34 da fara wasan, domin dan wasan Leicester City Wesley Fofana wanda musulmi ne da yake azumi ya samu damar yin buda baki, kafin ci gaba da wasan.

An tsayar da wasan ne a daidai lokacin da aka kira sallar Magriba, inda Fofana ya samu ruwa ya sha da kuma lemun kwalba, kafin daga bisani aka ci gaba da wasan, wanda kungiyar da Leicester City ce ta yi nasara a wasan, inda ta doke Crystal Palace da ci 2 da 1.

Bayan wasa na kimanin mintuna 60, ami horar da kungiyar kwallon kafa ta Leicester City Brendan Rodgers ya fitar da Fofana, inda ya canja shi da wani dan wasan.

Rodgers ya bayyana cewa ya fitar da Fofana ne domin ya samu ya huta, saboda a tsawon ranar bai ci komai saboda yana azumi, duk da cewa ya san Fofana dan wasa ne mai kokari wanda yake buga wasa mintuna 90 yana azumi ba tare da ya nuna wata gajiyawa ba.

Shi ma a nasa bangaren Fofana ya gode wa hukumar wasannan Premier League, kan yadda aka tsayar da wasa domin ba shi damar yin buda baki.

 

 

3967434

 

 

captcha