IQNA

Yahudawan Isra'ila 44 Suka Halaka Sakamakon Cunkoso A Wani Taronsu Na Addini A Yau Juma'a

23:32 - April 30, 2021
Lambar Labari: 3485861
Tehran (IQNA) akalla yahudawan Isra'ila 44 ne suka rasa ransu wasu kuma kimanin 150 suka samu raunuka sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a wani wurin ibadar yahuadawa a yau.

Rahotanni daga Isra'ila na nuni da cewa alal aƙalla mutane 44 me sun rasa ransu wasu kuma kimanin 150 suka samu raunuka sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a wani wurin ibada na yahudawa a safiyar yau Juma’a.

Cibiyar ba da agaji ta Isra’ilan ce ta sanar da hakan a yau ɗin nan inda ta ce alal aƙalla mutane 44 sun mutu yayin da ake gudanar da taron Ibadan kana wasu kuma da dama sun sami raunuka wasu ma raunukan na su sun yi tsanani.

Turmutsutun dai ya faru ne lokacin da dubbun dubatan masu ibada suka taru a kasan tsaunin Meron da ke arewacin Isra’ilan don gudanar da bikin na ibada, inda wani waje da ɗimbin mutane ke tsaye a kai ya karye wanda hakan ya haifar da turmutsitsin a ƙoƙarin ficewa daga wajen da mutane suke yi.

Wasu rahotannin sun ce wannan shi ne wani taro mafi girma da aka gudanar a Isra'ilan tun ɓullar annobar korona.

3968127

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yahudawan sahyuniya
captcha