IQNA

Musulmin Amurka Sun Raba Taimako Ga Mabukata A Kasar

23:52 - May 01, 2021
Lambar Labari: 3485866
Tehran (IQNA) Wata cibiyar musulmi da ke gudanar da ayyukan jin kai a kasar Amurka tana bayar da tallafi ga mabukata a fadin kasar.

Tashar Arab News ta bayar da rahoton cewa, tun daga farkon watan azumin ramadan, cibiyar musulmi da ke gudanar da ayyukan jin kai a kasar Amurka ta DoorDash, take gudanar da ayyukan jin kai ta hanyar bayar da tallafi ga mabukata a fadin kasar ta Amurka.

Khalil Damir shugaban kwamitin tattara zakka a kasar Amurka, kuma daya daga cikin masu tafiyar da cibiyar ta tallafi ya bayyana cewa, suna bayar da taimako na abinci da kayayyakin bukatar rayuwa ga mutanen da suke cikin bukata, ba tare da la’akari da addininsu ko akidarsu ba.

Ya ce suna gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwa da wata hukuam da ke gudanar da ayyukan raba kayan dauki ta kasa, wadda take taimaka musu wajen raba wadannan kayayyaki a cikin dukkanin jihohin kasar ta Amurka.

Ya kara da cewa, sun zabi wanann lokaci na azumin watan ramadan ne kasantuwar wata ne na rahma da jin kai ga talikai, kuma Allah yana ninka lada a kan kowane aiki na alhairi a cikin wannan wata mai alfarma.

Musulmin kasar Amurka dais una gudanar da irin wadannan ayyuka na alhairi ga sauran mutanen kasar wadanda ba musulmi, wanda hakan kuma yana yin gagarumin tasirin wajen kara fitowa da kyakkayawar koyarwa ta jin kan dam da addinin musulunci ya koyar da musulmi.

 

3968457

 

captcha