IQNA

'Yan Kasashen Ketare Za Su Sauke Farali A Bana

23:43 - May 10, 2021
Lambar Labari: 3485900
Tehran (IQNA) Saudiyya ta sanar da cewa, a shekarar bana maniyyata daga kasashen ketare za su samu damar sauke farali

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa, a shekarar bana maniyyata daga kasashen ketare za su samu damar sauke farali.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar, ma’aikatar kula da harkokin hajji da umrah a kasar Saudiyya ta sanar da cewa, a shekarar bana maniyyata daga kasashen ketare za su samu damar sauke farali, amma bisa tsari na musamman da aka yi kan hakan.

Bayanin ya ce tsarin ya hada da daukar kwararan matakai na kula da kiwon lafiya a yayin gudanar da aikin hajji, domin kauce wa yaduwar cutar corona a tsakanin mahajjata, duk kuwa da cewa an kayyade adadin mahajjatan da za su samu damar sauke farali a shekarar ta bana.

A shekarar da ta gabata dai mutane dubu 10 ne kawai suka samu damar sauke farali, da suka hada da ‘yan cikin kasar ta saudiyya, da kuma ‘yan kasashen waje wadanda suke cikin kasar ta Saudiyya a lokacin aikin hajjin, sabanin shekarar bana, inda za a bayar da dama ga wani adadi daga kasashen ketare domin su shigo kasar domin sauke farali.

An kiyasta cewa dai a shekarar bara gwamnatin saudiyya ta yi asarar kudi da suka kai dala biliyan 12 sakamakon rashin halartar alhazai daga kasashen duniya, wanda hakan yana daya daga cikin hanyoyin da kasar take samun kudaden shiga.

 

3970448

 

 

captcha