Tashar Alalam ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayaninsa da ya gabatar a yau dangane da halin da ake ciki a yakin da Isra’ila take kaddamarwa kan al’ummar Falastinu, Shugaban kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, Isra’ila ta raina karfin da kungiyoyin Falastinawa ‘yan gwagwarmaya suke da shi, amma bayan kaddamar da yakin da ta yi a yanzu ta fahimci sabanin abin da take tunani a baya.
A daya bangaren kuma a yau dakarun Qassam bangaren soji na kungiyar Hamas sun kaddamar da wani hari a yau a kan wata motar bas da take dauke da sojojin Isra’ila a kusa da shingen da Isra’ila ta kafa wanda ya raba yankin zirin Gaza, da sauran yankunan Falastinawa da ta mamaye.
Jim kadan bayan faruwar lamarin, wasu tankokin yankin Isra’ila suka turnuke wurin da hayaki, domin kada kamarori su iya daukar hakakinanin abin da ya faru da sojojin yahudawan.
Baya ga haka kuma da yammacin yau Alhamis, dakarun na Qassam da ma wasu kungiyoyin gwagwarmaya a Gaza, sun harba makamai masu linzami a kan wasu yankuna da Isra’ila ta mamaye, inda ta tsugunnar da yahudawa ‘yan share wuri zauna, wanda shi ma Isra’ila tana ci gaba da yin rufa-rufa kan hakan.