Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wannan aiki an cimma matsayar gudanar da shi tsakanin malaman addinan kiristanci, da yahudanci da kuma musulmi a kasar Jamus, wanda a wurin za a gina masallaci, da majami’ar kiristoci gami da wurin bautar yahudawa.
An cimma wannan matsayar ne a wata tattaunawar addinai da ake gudanarwa a Jamus, wadda take hada jagororin mabiya wadannan addinai, inda bakinsu ya zo daya a kan samu wani babban wurin wanda za a gina dukkanin wuraren ibada na wadannana ddinai a cikinsa.
An kiyasta cewa aikin ginin wurin zai lakume kudi har euro miliyan 47, amma a halin yanzu akwai miliyan 20 da aka tanada domin fara aikin, wanda daga bisani za a kammala hada sauran kudaden.
Jagororin mabiya addinin musulunci da kiristanci da yahudawa a kasar Jamus dai suna da kyakkyawar fahimta a tsakaninsu, wanda hakan yana taimakawa matuka wajen samun zaman lafiya a tsakanin mabiya wadannan addinai a kasar.