IQNA

Martanin Kungiyar Jihadul Islami Kan Kisan Matashi Musulmi Da Isra'ila Ta Yi A Nablus

22:39 - June 17, 2021
Lambar Labari: 3486020
Tehran (IQNA) kungiyar jihadul Islami ta mayar da martani dangane da kisan da Israi'ila ta yi wa wani matashi bafalastine.

Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, kungiyar jihadul Islami ta mayar da martani dangane da kisan da Israi'ila ta yi wa wani matashi bafalastine a yankin Jabal Sabih da ke cikin gundumar Nablus a Falastinu.

Kakakin kungiyar Jihadul Islami Tarik Salma ya bayyana cewa, irin matakan da Isra'ila take dauka domin murkushe matasan Falastinawa da suke hana ta yin kutse a cikin yankunansu, hakan ba zai yi tasiri ba, domin hakan shi ne ke kara karfafa gwiwar matasan wajen yin gwagwarmaya da zaluncin Isra'ila.

A jiya ne sojojin Isra'ila suka harbe Ahmad Bani Shamsa matashi dan shekaru 16 da haihuwa a kusa da garin nablus, a lokacin ad matasan suka hana sojojin yahudawa kutsa kai a cikin yankuannsu.

A nasa bangaren shugaban kungiyar Jihadul Islami Ziyad Nakhala ya bayyana cewa, matasan Falastinawa za su ci gaba da yin tsayin daka a gaban duk wani aikin wuce gona da iri da ta'addanci irin na Isra'ila, domin kuwa kisa ba ya tsorata matasan Falastinawa wajen kare hakkokinsu da al'ummarsu.

 

 

3978144

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tasiri ، matashi ، matashi bafalastine ، gundumar Nablus ، gwagwarmaya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :