Shafin yada labarai na Al-nashrah ya bayar da rahoton cewa, a yayin ziyarar ta tawagar Hamas Lebanon, Isma’il Haniyya a yau ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah a birnin Beirut fadar mulkin kasar ta Lebanon.
Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa daban-daban da suke da alaka da kawancen Hizbullah da kuma Hamas, da kuma yadda za su ci gaba da kara karfafa wannan kawance wajen gudanar da ayyukansu a bisa manufofi na gwagwarmaya da mamayar Isra’ila a yankunan larabawa.
Haniyya da Sayyid Nasrullah sun jaddada cewa, kawancen da ke tsakanin Hibulah da Hamas yana a matsayin kawance na sadaukarwa domin wanzuwar al’umma a cikin ‘yanci da daukaka.
Kafin wannan lokacin dai Isama’ila Haniyya ya gana da shugaban kasar Lebanon Micheil Aoun, bayan nan kuma ya gana da shugaban majalisar dokoki Nabih Birri da kuma Firayi minista Hassan Diyab.
Tuna cikin makon da ya gabata ne Tawagar ta Hamas ta fara gudanar da ziyara a wasu kasashen larabawan yankin arewacin Afirka, da suka hada da Mauritaniya da kuma Morocco, a wannan makon kuma baya ga kasar Lebanon, ziyarar za ta hada da kasashen Iran da kuma Turkiya.