IQNA

Haniyya: Zamu 'Yantar Da Quds Tare Da Taimakon Allah Da Kuma Al'ummar Musulmi

22:59 - July 01, 2021
Lambar Labari: 3486067
Tehran (IQNA) Shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasɗinu Hamas ya bayyana cewa da taimakon Allah da na al'ummar musulmi za a 'yantar da masallacin Quds.

Shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasɗinu, Hamas, malam Isma’il Haniya ya bayyana cewar dakarun gwagwarmaya suna da wasu ƙarfafan hanyoyi da za su iya amfani da su wajen tsorata Isra’ila da kuma hana ta ɗaukar matakan cutar da al’ummar Falasɗinu.

Malam Haniya ya bayyana hakan ne a ƙasar Labanon inda ya ke ci gaba da ziyara ta kwanaki a ƙasar don ganawa da jami’an ƙasar ta Labanon da kuma jami’an ƙungiyoyin gwagwarmaya da suke ƙasar.

Yayin da ya ke magana kan yaƙin kwanaki 11 da Isra’ila ta ƙaddamar kan al’ummar Gazan da kuma nasarar da dakarun gwagwarmayar suka samu kan sahyoniyawan inda ya ce dakarun gwagwarmayar suna da ƙarfin da za su iya sanya Isra’ilan ta sake tunani a duk lokacin da take son ɗaukar wani mataki na cutar da al’ummar Falasɗinun.

Shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar ta Hamas ya ƙara da cewa wannan yaƙin yayi sanadiyyar haɗin kan dukkanin al’ummar Falasɗinu waje guda, shin waɗanda suke cikin gida ne ko kuma waɗanda suke waje,da kuma zaɓan tafarkin gwagwarmaya a matsayin hanya guda ta faɗa da wuce gona da irin Isra’ila.

Har ila yau kuma Malam Haniya ya gana da babban sakataren ƙungiyar Jihadi Islami, Ziad al-Nakhalah, wacce ita ma ƙungiyar ta taka gagarumar rawa yayin wannan yaƙin inda suka tattanawa kan batutuwa daban-daban ciki kuwa har da yadda za a ci gaba da aiki tare tsakanin ƙungiyoyin biyu.

Kafin hakan ma Haniya ya gana da babban sakataren ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon ɗin Sayyid Hasan Nasrallah inda yayi masa bayanin haƙiƙanin abubuwan da suka faru yayin yaƙin na Gaza da kuma hanyoyin da ƙungiyoyin biyu za su ci gaba da ƙarfafa alaƙa ta gwagarmaya da ke tsakaninsu.

Abubuwan Da Ya Shafa: ziyara shagaban hamas
captcha