IQNA

Saudiyya Ta Sanar Da Ranar 20 Ga Watan Yuli A Matsayin Ranar Idin Babban Sallah

18:55 - July 10, 2021
Lambar Labari: 3486090
Tehran (IQNA) mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da ranar 20 ga watan Yulin da muke ciki a matsayin ranar idin babbar sallah.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da gwamnatin Saudiyya ta fitar, ta bayyana ranar 19 ga Yulin da muke ciki a matsayin ranar Arafa, sannan kuma 20 ga watan Yuli a matsayin ranar idin babbar sallah.

Bayanin ya ce, sakamakon yadda aka duba jinjirin watan Zulhijjah a ranar jiya Juma'a amma ba a ga watan ba, a yau Asabar 29 ga watan Zulqaadah, ita ce ranar karshe ta wannan wata, gobe Lahadi tana a matsayin daya ga watan Zulhijjah.

Haka nan kuma hukumomin na Saudiyya sun bayyana cewa,  a yau ma za a kara yin dubar jinjirin watan Zulhijjah, amma bisa ga lissafi yau Asabar yau ce ranar karshe ta watan Zulqaadah.

 

3982919

 

 

captcha