IQNA

Kungiyar Barcelona Ta Faranta Wa Falastinawa Saboda Kin Yin Wasa Da Wata Kungiyar Kwallo Ta Isra'ila

20:59 - July 18, 2021
Lambar Labari: 3486116
Tehran (IQNA) Falastinawa sun gode wa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona saboda kin yin wasan sada zumunci da wata kungiyar kwallon kafa ta Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, hukumar wasannin kwallon kafa ta Falastinu, ta gode wa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona saboda kin yin wasan sada zumunta da wata kungiyar kwallon kafa ta Isra'ila.

A cikin wani bayani da ya fitar, shugaban hukumar kwallon kafa ta Falastinu Jiril Rajub ya bayyana cewa, al'ummar Falastinu sun yi farin ciki da matakin da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dauka, na kin amincewa ta gudanar da wasan sada zumunci da kungiya da kungiyar kwallon kafa ta Bitar ta yahudawan sahyuniya.

Ya ce wannan mataki ne na jarunta wanda ya cancanci yabo daga dukkanin al'ummar Falastinu da sauran musulmi, da ma dukkanin masu 'yanci da 'yan adamtaka a duniya.

Rajabu ya kara da cewa, tun kafin wannan lokacin Barcelona ta sha daukar matakai na nuna goyon bayan ga al'ummar falastinu, da kuma nuna 'yan adamtaka a cikin lamurra da dama da suke faruwa a duniya.

A jiya ne shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bitar Moshe Hugig ya sanar da cewa, Barcelona ta yi watsi da gayyatar da kungiyar kwallon kafan ta yahudawa na neman a buga wasan sada zumunta  a tsakaninsu, wanda aka tsara zai gudana a ranar 4 ga watan agusta mai kamawa.

 

3984829

 

 

 

captcha