IQNA

23:44 - July 28, 2021
Lambar Labari: 3486149
Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da baiwa Isra’ila kujera a matsayin mamba mai sanya ido a kungiyar tarayyar Afirka.

A cikin wani bayani da ma’aikatar kula da alakoki na kasa da kasa ta kasar Afirka ta kudu ta fitar, ta bayyana cewa, matsayar da kungiyar tarayyar Afirka ta dauka na bai wa Isra’ila kujera a matsayin mamba mai sanya ido, hakan abin Allawadai ne.

Bayanin ya ce, kungiyar tarayyar afirka ta dauki wannan matakin ne bisa ra’ayin wasu, amma ba bisa ra’ayin dukkanin kasashen Afirka ba, kuma yin hakan yana a matsayin halasta ayyukan zaluncin Isra’ila a kan al’ummar Falastinu ne.

Ita a nata bangaren kasar Aljeriya ta bayyana cewa, ta yi takaici matuka dangane da wannan mataki da kungiyar tarayyar Afirka ta dauka, domin kuwa a cewar gwamnatin Aljeriya, ba a yi doguwar shawara tare da dukkanin mambobi na kungiyar ba.

Bayanin gwamnatin kasar ta Aljeriya ya kara da cewa, wannan mataki ya yi hannun riga da matakin kungiyar tarayyar Afirka na shekaru ba, wanda kuma akan wannan matakin ne siyasar kungiyar ta kafu, na nun goyon bay aga al’ummar Falastinu, da kuma kin amincewa da duk wani nau’in zalunci na Isra’ila a kan al’ummar Falastinawa

Tun fiye da shekaru 20 da suka gabata ne Isra’ila ke ta fadi tashin ganin ta samu zama mamba ‘yar kallo a kungiyar tarayyar Afirka, amma ba ta samu hakan ba sai a yanzu.

Jakadan gwamnatin yahudawan Isra’ila a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ne zai zama wakilin Isra’ila a kungiyar tarayyar Afirka, inda a jiya ya mika takardunsa ga shugaban kwamtin zartarwa na kungiyar .

 

3987077

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kungiyar tarayyar Afirka ، zama mamba ، Addis ababa ، halasta
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: