IQNA

An Damke Daya Daga Cikin Masu Hannu Wajen Kai Wa Magoya Bayan Hizbullah Hari

22:54 - August 02, 2021
Lambar Labari: 3486162
Tehran (IQNA) jami'an tsaron Lebanon sun samu nasarar cafke daya daga cikin wadanda suka kai wa janazar wani dan Hizbullah hari.

Shafin Sharq al-ausat ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron Lebanon sun samu nasarar cafke daya daga cikin wadanda suka kai wa janazar wani dan Hizbullah hari a jiya.

Bangaren ayyukan asiri na soji a kasar Lebanon ya sanar da cewa, an samu nasarar kame daya daga cikin mutanen ad suka kai harin ne a lokacin da ake janazar daya daga cikin dakarun Hizbullah da wasu suka kashe shi a ranar Asabar da ta gabata.

Bayanin jami'an tsaron ya ce waanda suka yi hakan za su fuskanci shari'a domin fuskantar hukuncin abin da suka aikata, musamman ma ganin cewa a lokacin janazar sun kuma sake kashe wasu mutane uku.

Kungiyar Hizbullah ta ce ba za ta yi komai kan hakan ba, amma dole ne a kan jami'an tsaro su kama duk wanda yake da hannu cikin lamarin kuma ya fuskanci shari'a.

 

 

3988089

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: cafke ، samu nasarar ، janazar ، Hizbullah
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha