IQNA

Aljeriya Da Wasu Kasashe Na Kokarin Ganin An Kwace Kujerar Da Aka Bai Wa Isra'ila A AU

19:53 - August 04, 2021
Lambar Labari: 3486169
Tehran (IQNA) Wasu daga cikin kasashen Afirka sun yi watsi fatali da batun baiwa Isra’ila kujera a matsayin mamba mai sanya ido a kungiyar Tarayyar Afirka.

Wasu daga cikin kasashen Larabawan Afirka na kokarin ganin an kwace kujerar da aka bai wa Isra’ila a matsayin mamba mai sanya ido a kungiyar tarayyar Afirka.

Haka nan kuma ba ga wadannan kasashe akwai wasu daga cikin kasashen da ake sa ran za su goyi bayan wannan matsaya da wadannan kasashen suka dauka, daga cikin kasashen akwai Gabon, Senegal, Mali, Nijar, Najeriya, Tanzania, Afirka ta Kudu, Zimbabwe, Iretrea.

Tun kafin wannan lokacin wasu daga cikin wadannan kasashe sun nuna rashin gamsuwarsu da wannan mataki, musamman kasar Afirka ta kudu, wadda ta fito a hukuamnce ta yi Allawadai da hakan, tare da bayyana shi a matsayin halasta zaluncin Isra’ila a kan al’ummar Falastinu.

Kamar yadda ita ma gwamnatin Aljeriya ta bayyana cewa, an yanke hukuncin yin hakan ne kawai ta hanyar daukar ra’ayoyin wasu, amma ba ra’ayin dukkanin kasashe mambobi na kungiyar ba.

A kan haka Aljeriya ta ce ba za ta taba goyon bayan baiwa Isra’ila kujera a matsayin mamba ‘yar kallo a cikin kungiyar tarayyar Afirka ba, domin kuwa yin hakan ya yi hannun riga da manufofin siyasar kungiyar, wadanda suka ginu a kan kare hakkokin bil adama a duk inda suke a duniya.

 

3988321

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha