IQNA

Za A Gudanar Da Canjin Tutar Hubbaren Imam Hussain (AS) Ba Tare Da Taron Jama'a Ba

22:20 - August 09, 2021
Lambar Labari: 3486184
Tehran (IQNA) a shekarar bana za a gudanar da canjin tutar hubbaren Imam Hussain (AS) ba tare da taron jama'a ba.

A shekarar bana za a gudanar da aikin canja tutar hubbaren Imam Hussain (AS) ba tare da halartar jama'a ba kamar yadda aka saba yi  kowace shekara.

Akil Sharifi daraktan watsa labarai na hubbaren Imam Hussain (AS) ya bayyana cewa, bisa la'akari da cewa yanayin da ake ciki a bana ya banbanta sauran yanayi a baya, hakan yasa dole a dauki matakai da suka dace domin rage cunkoson jama'a.

Ya ci gaba da cewa, a kowace shekara ana canja tutocin hubbarori biyu da suke Karbala na Imam Hussain (AS) da kuma Abul Fadl Abbas (AS) tare da halartar dubban jama'a, wanda kuma bana sabanin haka ne.

Sannan kuma ya bayyana cewa irin wadannan matakai za su shafi sauran bangarori na taruka, domin tabbatar da cewa an kiyaye ka'idoji na kiwon lafiya a yayin tarukan juyayin Ashura da za a gudanar nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

 

3989452

 

captcha