IQNA

Sadaukarwar Ashura Ta Shata Makoma Ga 'Yancin 'Yan Adam

22:57 - August 10, 2021
Lambar Labari: 3486189
Tehran (IQNA) lamarin sadaukarwa a waki'ar Ashura ya shata makoma ne ga 'yan adam da kuma 'yan adamtaka.

A zanatwa da kamfanin dillancin labaran iqna, Sheikh Muhammad Hadi Fakhruddin malami a kasar Iran ya bayyana cewa, lamarin waki'ar Ashura ya shata makoma ne ga 'yan adam da kuma 'yan adamtaka.

Ya ci gaba da cewa, lamarin Ashura yana yin ishara ne da sadaukarwa saboda wani abu da aka yi imani da shi na gaskiya, da kuma imani da makoma ta hakika.

Sadukarwa ce a tafarkin gaskiya wajen kokarin kawar da bata da barna da kuma gurbatar da addinin Allah, da halakar da bayin Allah.

Wannan sadaukarwa tana da asali a cikin addinin Allah, domin kuwa manzon Allah (SAW) shi ne shugaban masu sadaukarwa a tafarkin Allah, saboda haka kuma alayensu su ne suka fi cancantar sadaukarwa a bayansa, domin kuwa da su ne ake yin koyi matukar ana son abi koyarwar manzon Allah ta hakika.

Wannan shi ne babban sirrin wannan sadaukarwa wadda mafi daukakar matsayi a cikin halittun ubangiji a bayan kasa a wannan lokaci, mafi soyuwa ga Allah a kan dukkanin bayinsa a lokacin, limamin ahlul bait wato alayen manzon Allah Imam Hussain (AS) ya jagoranci wannan sadaukarwa domin kare addinin Allah wanda kakansa ya zo da shi kuma ya isar da shi ga 'yan adam.

Tun daga wancan lokacin, wannan sadaukarwar ta shata wani bayyanannan layi na banbamcewa tsakanin gaskiya da karya, shiriya da bata, ilimi da jahilci, tsoro da kuma jarunta, kokwanto da kuma sakankancewa.

A ta fuskar 'yan adamtaka kuwa, sadaukarwar Imam Hussain (AS) da alayen manzon Allah (SAW) a ranar Ashura, ta zama wani alami na sadaukarwa domin rayuwa cikin 'yanci, ko mutuwa a kan manufa a cikin daukaka, amma dai ba mika wuya ga mabarnata da rayuwa cikin kasakanci ba.

 

3989627

 

 

 

captcha