IQNA

Mutane Miliyan 5 Ne Suka Halarci Taron Juyayin Ashura A Birnin Karbala

21:49 - August 20, 2021
Lambar Labari: 3486222
Tehran (IQNA) masu ziyara miliyan 5 suka halarci taron juyayin Ashura a birnin Karbala na kasar Iraki wanda ya gudana a jiya.

Bangaren yada labarai na hubbaren Imam Hussain (AS) ya sanar da cewa, masu ziyara miliyan 5 suka halarci taron juyayin Ashura a birnin Karbala na kasar Iraki wanda ya gudana a jiya Alhamis.

Haka nan kuma bayanin ya ce, 'yan jarida 400 daga kafofin yada labarai daban-daban na ciki da wajen kasar Iraki suka halarci domin bayar da rahotanni.

Bayanin ya ce an gudanar da tarukan juyayin Ashura cikin nasara kamar yadda aka shirya su ba tare da samun wata matsala ba, kamar yadda aka aiwatar da tarukan bisa tsarin kiwon lafiya da aka yi saboda matsalar cutar corona.

Haka nan kuma a bangaren tsaro jami'an tsaro sun yi aikinsu kamar yadda ya kamata, domin bayar da kariya ga masu da suka halrci wurin tarukan na birnin Karbala, wadanda suka hada da mutanen cikin kasar ta Iraki da kuma baki daga kasashen ketare.

 

3991886

 

captcha