Tashar talabijin ta Alkafil ta bayar da rahoton cewa, kamar yadda aka saba yi a kowace shekara a daidai rin wannan lokaci, a bana ma an gudanar ad taron karatun kur'ani mai tsarki a hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin Karbala na kasar Iraki,tare da halartar daruruwa makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki.
Baya ga karatun kur'ani mai tsarki, aka gudanar da wakoki na yabon manzon Allah (SAW) da Ahlul bait nasa, musamman limaman ahlul bait (AS) daga cikinsu kuwa har da Imam Hussain (AS).
Sannan kuma sukan yi tattaki tsakanin hubbaren Imam Hussain (AS) da kuma hubbaren dan uwanda Abbas (AS) wanda yake da 'yar tazara kadan daga hubbarensa.
Taron ya gudana a cikin tsari na kiwon lafiya, bayan yin feshin magunguna da kuma daukar matakai wadanda za su taimaka wajen hana yaduwar cututtuka musamman korona da ake fama da ita.