IQNA

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce A Shirye Yake Ya Yi Aiki Da Sabuwar Gwamnatin Iran

19:14 - September 01, 2021
Lambar Labari: 3486259
Tehran (IQNA) Antonio Guterres ya bayyana bukatar yin aiki da Iran domin tabbatar zaman lafiya da tsaro da ci gaba mai daurewa.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana bukatar yin aiki da Iran domin tabbatar zaman lafiya da tsaro da ci gaba mai daurewa a fadin duniya.

A wata wasika da ya aike wa shugaban kasar ta Iran Ibrahim Ra’isi, babban sakataren na MDD, ya taya zababben shugaban kasar ta Iran murna akan zabin da akayi masa, tare da fatan yin aiki tare da sabuwar gwamnatin ta Iran.

Guterres ya kara da cewa, ’shugabancin ka ya zo a daidai wani lokaci mai tsanani a fadin duniya, inda ake fama da annobar korona, canjin yanayi da rikice rikice suka mamaye duniya ciki har da a yankin gabas ta tsakiya’’.

Saboda haka babban sakataren na MDD, ya bayyana fatansa ga shugaban kasar ta Iran, na yin aiki tare, domin cimma burin da aka sanya a gaba na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da ci gaba mai daurewa da kare hakkin dan adam a duniya baki daya.

 

3994148

 

 

captcha