Kamfanin dillancin labaran kasar Habasha ENA ya bayar da rahoton cewa, 'yan tawayen Tigray sun yi amfani da manyan makamai wajen yin harbe-harbe da hakan ya yi sanadiyyar rushewar tsohuwar majami'ar tarihi ta (Chchhv Madnlyam) da ke Gondar ta kudu a cikin Lardin Amhara.
An gina wannan coci ne tun a cikin karni na uku miladiyya, wato kimanin shekaru dari uku kafin zuwan addinin muslunci.
Merigita daya ce daga cikin masu kula da wannan majami'a da aka gina shekaru dubu daya da dari takwas da suka gabata, wadda ta bayyana cewa 'yan tawayen Tigray sun yi ta harba makaman roka a kan wannan majami'a.
Ta ce wannan ya yi sanadiyyar rushe wasu bangarori na ginin wannan majami'a, wanda kuma hakan ya sanya wasu daga cikin kayan tarihin da suke cikinta sun lalace baki daya ta yadda ba za a iya gyara su ba, bayan suna cikin wurin fiye da shekara dubu daya da daruruwans hekaru wania bu bai taba samunsu ba.