IQNA

An Fara Shirin Tarbar Baki Domin Ziyarar Arba'in A Iraki

20:20 - September 09, 2021
Lambar Labari: 3486290
Tehran (IQNA) an fara shirin tarbar baki masu shirin gudanar da ziyarar arba'in na Imam Hussain (AS) a Iraki

Bangaren yada labarai na hubbaren Imam Hussain (AS) ya sanar da cewa, an fara shirin tarbar baki masu shirin gudanar da ziyarar arba'in na Imam Hussain (AS) a wannan shekara.

Shugaban kwamitin kula da shirya taruka a hubbaren Imam Hussain (AS) Sayyid Sadeq Samir Alyasiri ya bayyana cewa, an fara shirin tarbar masu ziyara kamar yadda aka saba yi a kowace shekara.

Ya ce kamar shekarar bara, a shekarar bana ma dukkanin shirye-shiryen suna kasancewa ne bisa tsauraran matakai na kiwon lafiya, sakamakon yaduwar cutar corona.

Baya ga haka kuma ya bayyana cewa, an yi tsare-tsare a bangaren yadda tarukan za su kasance da kuma da kuma wuraren hutuwa ga matafiya da suke shigowa Karbala daga bangarori daban-daban na birnin.

Ya ci gaba da cewa, dangane da matakan tsaro kuwa, tun daga lokacin tarukan Ashura da aka gudanar sama da wata guda da ya gabata, har yanzu dubban jami'an tsaro suna cikin shiri a dukkanin sassa na birnin da kuma hanyoyin da ke isa birnin daga birane daban-daban na kasar Iraki.

 

 

3996108

 

Abubuwan Da Ya Shafa: wannan shekara hubbaren imam hussain
captcha