IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Garkame Masallacin Annabi Ibrahim

19:23 - September 22, 2021
Lambar Labari: 3486340
Tehran (IQNA) Yahudawan Sahyuniya sun rufe masallacin Annabi Ibrahim (AS) tare da hana musulmi gudanar da ayyukan ibada a cikinsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar Aljazeera cewa, tun a yammacin jiya Talata, Yahudawan Isra’ila suka rufe masallacin Annabi Ibrahim (AS) da ke birnin Khalil a Falastinu, tare da hana musulmi gudanar da ayyukan ibada da salloli a cikin masallacin.

Shugaban kwamitin masalalcin Sheikh Hifzi Abu Saninah ya bayyana cewa, yahudawan sun garkame masallacin Annabi Ibrahim ne tun daga lokacin faduwar rana a jiya, inda suka hana yin sallar magariba a cikin masalalcin, daga lokacin kuma har zuwa yau yahudawan suna cikin masallacin.

Y ace yahudawan sun kutsa kai a cikin wannan masallaci ne tare da keta alfarmarsa, da sunan gudanar da bukukuwan idin yahudawa, wanda suke yi a kowace shekara a wannan lokaci, wada ake sa ran mai yiwa bayan kammala idin nasu su fice daga masallacin.

Tun a cikin shekara ta 1994 yahudawan suka fara yin wannan kutse a  cikin masallacin Annabi Ibrahim da sunan gudanar da bukukuwan yahudawa na shekaras-shekara.

Birnin Khalil na gabar yamma da kogin Jordan ne, sannan kuma akwai matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna guda 400 a gefensa da gwamnatin Isr’ila ta gina, inda sojojin Isra’ila ke gadinsu dare da rana.

 

3999297

 

 

 

 

captcha