IQNA

Wurin Da Ake Koyar Da Mata Karatun Kur'ani A Cikin Masallacin Quds

17:37 - October 05, 2021
Lambar Labari: 3486389
Tehran (IQNA) masallacin Qubbatu Sakhrah da ke cikin harabar masallacin Quds ya zama wurin koyar da mata karatu kur'ani

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daga arewa zuwa kudancin Palasdinu, daga tsaunuka da filayen da gabar tekunta, matan Falasdinawa suna zuwa Masallacin Aqsa don yin sallah, karatun Alkur’ani da halartar da’irar kimiyya.
 
Matan Falasdinawa sukan taru a da'irori da ke ake yi domin koyar da karatun kur'ani da sauran ilmomi na addinin mulsunci.
Masallacin Qubbatu Sakhrah gini ne mai kusurwa huɗu a cikin Masallacin Al-Aqsa wanda ke da tulluwa ta zinariya.
 
Wannan tulluwa ana ɗaukarta a matsayin wata alama a yankin baki ɗaya kuma tana ɗaya daga cikin tsoffi manyan abubuwan tarihi na Musulunci.
 
Samira wata mata ce da ta zo Masallacin Al-Aqsa daga birnin Acre a yankunan da aka mamaye a 1948 kuma ta ce a koyaushe tana ɗokin halartar ɗakin addu'ar, saboda wannan shi ne wurin da Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa, ya yi mi'iraji zuwa sama.
 
 

4001920

 

captcha