Jaridar Arabi Post ta bayar da rahoton cewa, wani babban jami'in gwamnatin Iraki da ke halartar tattaunawar da ake yi a tsakanin Iran da Saudiyya wadda Iraki ke jagoranta, ya ce an bijiro da batun gina hanya da za ta hada biranan Mashhad na Iran, Karbala na Iraki, da kuma Makka da ke kasar Saudiyya.
Jami'in ya ce, dukkanin bangarorin biyu na Iran da Saudiyya, sun yi lale marhabin da babban ci gaban da aka samu sakamakon tattaunawar da suke yi.
Firayi ministan kasar Iraki Musatafa Alkazimi ya bayyana cewa, kasashen Iran da Saudiyya a matsayinsu an manyan kasashe masu tasiria gabas ta tsakiya, za su bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban yankin a dukkanin bangarori.
Tun bayan samun sauyin gwamnati da aka yi a kasar Amurka, da kuma yadda gwamnatin Joe Biden ta fara juya wa wasu daga cikin kasashen larabawa baya, hakan yasa da dama daga cikin kasashen larabawa da a baya ba su dasawa da Iran, a halin yanzu sun fara shiga tattaunawa tare da ita.