Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, ayan kammala gasar kur'ani ta sheakara-shekara a karo na goma, an girmama mahardata kur'ani 100 a birnin Iskandariyya na kasar Masar.
Wannan dai shi ne karo na goma da ake gudanar da wannan gasa wadda take hada mahardata daga sassa na lardin Iskandariyya.
Gwamnan lardin Iskandariyya ne da kansa tare da halartar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnati da kuma malamai, ya gabatar da wadannan kyautuka ga mahardata kur'ani sun 100.
A lokacin da yake gabatar da jawabi, ya bayyana cewa babban abin alfahari ne yadda ake samun gagarumin ci gaba ta fuskar mayr da hankali ga kur'ania tsakanin matasa a lardin, ya yi godiya ga iyaye da suke dora 'ya'yansua a kan tarbiya ta kur'ani mai tsarki, da kuma malaman da suke koyar da yaran.