Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bukaci hukumomin Afghanistan dasu yi duk abunda ya dace domin hukunta wadanda ke da hannu a harin ta’addancin ranar Juma’a da aka kai kan wani masallacin lardin Kunduz.
‘’ Abun da ya faru ga masu ibada a masallacin Khanabad dake lardin Kunduz, abun takaici ne da kuma allawadai’’, kamar yadda jagoran ya bayyana a cikin wani sakonsa.
Kuma ya kamata ‘yan uwanmu makobtanmu, su dauki duk matakin da ya dace domin domin hukunta wadanda ke da hannu a wani harin, tare da daukan matakan kaucewa aukuwar irin hakan nan gaba, a cewar jagoran.
Ya kuma isar da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya rusa dasu.