IQNA

Babbar Cibiyar Fatawa Ta Kasar Masar Ta Jaddada Cewa Tawassuli Da Manzon Allah (SAW) Halastacce Ne A Shari'a

20:18 - October 27, 2021
Lambar Labari: 3486483
Tehran (IQNA) babbar cibiyar fatawa ta kasar Masar ta jaddada cewa tawassuli da manzon Allah da manzon Allah (SAW) domin biyan bukata a wurin Allah ya halasta a Shari'a.

Shafin jaridar Alwatan ta kasar Masar ya bayar da rahoton cewa, babbar cibiyar fatawa ta kasar Masar wato Darul Ifta, ta jaddada cewa tawassuli da manzon Allah (SAW) ya halasta a shari'a.

Wannan babbar cibiya ta fikihun Ahlu Sunnah ta duniya ta bayar da fatawar cewa, bai halasta musulmi ya yi musun halascin tawassuli da manzon Allah (SAW) domin kuwa halascinsa ya tabbata a shari'a.

Cibiyar ta kawo hadisan da wasu daga manyan masu ruwaito hadisai na ahlu sunnah suka ruwaito, daga cikinsu har da Tirmizi, da Ibn Majah.

Hadisin yana magana ne akan wani makaho da ya zo wurin manzon Allah (SAW) ya nemi da ya roka masa Allah domin ganinsa ya dawo, sai manzon Allah ya ba shi wata addu'a, wadda a cikinta ya ce ya roki Allah da ya dawo masa da ganinsa albarkacin manzonsa Muhammad, kuma ya roki Allah da hakan, kuma ganinsa ya dawo.

 

 

4008195

 

Abubuwan Da Ya Shafa: halasta ruwaito hadisai makaho
captcha