Kucher Umar Ali, fitaccen makarancin kur'ani ne kuma likitan yara daga garin Sulaimaniya a yankin Kudistan na kasar Iraki.
A cikin wannan faifan bidiyon da ya yi karatun kur'ani domin makon hadin kai a lokacin gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) ya karanta aya ta 1 zuwa ta 7 a cikin surat Qalam, da ke bayani kan kyawawan dabi'u irin na manzon Allah (SAW).
An haifi Kucher Umar Ali a yankin Kurdistan na Iraki a shekarar 1982, kuma ya yi karatun likitanci, daga bisani kuma ya koma ya kware a kan likitan kananan yara, a lokaci guda kuma yana gudanar da harkokinsa na kur'ani.