IQNA

An Bude Cibiyar Tattaunawa Tsakanin Addinai A Majami'ar Orthodox Ta Kasar Masar

14:45 - November 08, 2021
Lambar Labari: 3486527
Tehran (IQNA) An kaddamar da Cibiyar Nazarin Addini da Tattaunawa tsakanin addinai tare da halartar dimbin mabiya addinin kirista na Masar a Cocin Margerides Ortodoks da ke Masar.

An kaddamar da cibiyar ne a tare da halartar Sami Fawzi, shugaban majami’ar dioceses ta Alexandria a cocin Anglican Episcopal da Theodore II, babban malamin addinin Kiristanci na Orthodox 
 
Sami Fawzi, yayin da yake magana kan bude cibiyar nazari da tattaunawa tsakanin addinai, ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta ayyukan tattaunawa tsakanin addinai. 
 
Ya kara da cewa: "Majami'ar Episcopal tana kokarin bude "Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci da Kiristanci" Matran Munir Hana, wanda kuma wannan kokarin da Cocin ta Masar ta yi na yin karatun Islama da Kirista a lokaci guda, zai karfafa alaka tsakanin Musulunci da Kiristanci da karin fahimtar juna.
 

4011465

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: coci
captcha