IQNA

Bagheri: Tattaunawar Vienna Za Ta Mayar Da Hankali Ne Kan Cire Wa Iran Takunkumi

17:08 - November 12, 2021
Lambar Labari: 3486544
Tehran (IQNA) tattaunawar da za a gudanar a Vienna tsakanin Iran da kasashen turai, za ta mayar da hankali ne kan batun cire wa Iran takunkuman da Amurka ta kakaba mata.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Baqeri-Kani ya bayyana cewa, tattaunawar da za a gudanar a Vienna tsakanin Iran da kasashen turai, za ta mayar da hankali ne kan batun cire wa Iran takunkuman da Amurka ta kakaba mata.
 
Babban jami'in diflomasiyyar na Iran ya ce yana da muhimmnci ga dukkan bangarorin su koma ga alkawuransu, domin hakan shi ne kashin bayan samun nasarar tattaunawar.
 
Yanzu haka Baqeri-Kani yana gudanar da ziyara a wasu kasashen turai, da suka hada da Faransa, Jamus, inda a yau Alhamis kuma ya isa birnin landan na kasar Burtaniya, inda yake tattaunawa jami’an gwamnatocin wadannan kasashe, a matsayin share fagen tattaunawar ta Vienna.
 
A wata hira da ya yi da gidan radiyon Jamhuriyar Musulunci ta Iran Baqeri-Kani ya ce tattaunawar da za a yi na kwamitin hadin gwiwa ba za ta kasance kan batun nukiliya da aka riga aka cimmawa ba, domin an riga an warware wannan batu, a kan hakan abu mafi muhimmanci shi ne mayar da hankali kan ficewar Amurka daga yarjejeniyar da kuma yadda za ta dawo ta yi aiki da abin da ke cikinta, da janye takunkuman da ta kakaba wa Iran.
 

 

4012495

 

captcha