IQNA

An Sanar Da Sakamakon Gasar Kur'ani Ta Duniya Ta Mata Ta Dubai

21:21 - November 28, 2021
Lambar Labari: 3486615
Tehran (IQNA) an sanar da sakamakon gasar kur'ani ta duniya ta mata zalla da aka gudanar a birnin Dubai na UAE.
Shafin Al raya ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya ne aka kammala ayyukan gasar ur'ani ta mata ta kasa da kasa karo na biyar a Dubai, tare da bayar da lambar yabo ta matan Dubai mai suna "Sheikh Fatemeh Bint Mubarak".
 
Kuma a yayin rufe gasar an girmama dukkanin wadanda suka lashe gasar su 10 da dukkan wadanda suka halarci gasar daga kasashe 50, da wadanda suka  al'ummominsu.
 
Mahalarta gasar sun shafe kwanaki shida suna fafatawa a gaban kwamitin alkalai na kasa da kasa wanda ya kunshi fitattun shehunai da malamai masu gogewa wajen yin hukunci.
 
 

4016797

 

captcha