IQNA

'Yan Majalisar Burtaniya Musulmi Sun Soki Gwamnati Kan Nuna Ko In Kula Kan Kyamar Musulmi

21:26 - December 01, 2021
Lambar Labari: 3486629
Teahran (IQNA) ‘Yan majalisa musulmi a kasar Birtaniya sun yi kakkausar suka kan yadda gwamnatin kasarke nuna halin ko in kula kan nuna kyama ga musulmi a kasar.

A cewar jaridar Telegraph, da dama daga cikin wakilan musulmin Birtaniya da suka yi imanin cewa ba za a iya yakar wani abu da ba a fayyace shi ba, sun yi kira ga gwamnatin Birtaniyya da ta samar da ma’anar kyamar Musulunci.

A wani zama da majalisar dokokin Birtaniyya ta gudanar a bisa shawarar dan majalisar jam'iyyar Labour Afzal Khan, wakilan musulmi sun bayyana munanan abubuwan da suka faru na kiyayyar da suka fuskanta, tare da sukar gwamnati saboda gazawarta.

Naz Shah, Wakilin Bradford West Naz Shah ya ce "Nuna kymar Musulunci yana zama ruwan dare a cikin al'ummar Burtaniya, kuma gwamnati ba ta daukar hakan da muhimmanci." Gwamnati ba ta damu ba, shi ya sa lamarin ke kara tsananta.

A cikin watan Nuwamban 2018,  jam'iyyu da yawa a Majalisar Dokokin Burtaniya sun yi ta ba da shawarar a fitar da ma'anar kyamar Islama abin da hakan ke nufi, inda suke bayar da mahanrsu a kan cewa, "Kiyayya da musulunci ta samo asali ne daga wariya."

Wannan ma'anar kyamar addinin Islama da wasu suka gabatar a haka, ta samu karbuwa daga Jam'iyyar Labour, da Federal Liberal Democrats da magajin garin Landan, da ma kananan hukumomi da dama, inda su ma suke ganin ya kamata a dau matsaya guda kan haka, tare da fitar da doka ta shari’a wadda za a iya yin hukunci a kanta har ma dauri ga duk wanda ya aikata hakan.

 

4017618

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kyamar musulmi kasar Burtaniya
captcha