IQNA

Hizbullah: Sirrin Karfi Da Nasarorinmu Shi Ne Dogaro Da Allah

23:34 - December 06, 2021
Lambar Labari: 3486652
Tehran (IQNA) Sayyid Safiyuddin shugaban mjalisar zartarwa ta kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, babban sirrin karfi da nasarorin kungiyar shi ne dogaro da Allah.

Shafin yada labarai na Al-ahad ya bayar da rahoton cewa, Shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce wasu na ganin takunkumin kasashen turai kan kungiyar zai iya raunana tsayin dakanta.

Sayyid Hashem Safiyuddin, ya jaddada cewa: Idan wasu suna ganin za su iya raunana tsayin daka ta hanyar takunkumi, ko kuma zabe, zan gaya musu cewa kuna yin kure a tunaninku.
 
Baku karanta tarihin mu ba, kuma ba ku san hakikanin mu ba kuma har yanzu ba ku san sirrin da cikin tsayin daka da wanzuwarmu ba, domin sirrin shi ne dogara ga Allah madaukakin sarki.
 
Ya kara da cewa, har kullum masu adawa da kungiyar da suke hankoron ganin bayanta, a ciki ne ko kuma a wajen kasar, suna kallon lamarin kungiyar ne kawai ta mahanga guda, shi ne ta fuskacin abin da suke gani a kasa, wato karbuwar kungiyar da kuma nasarorinta a duk abin da ta sanya a gaba, alhali duk hakan yana faruwa ne tare da taimakon Allah.
 

4018862

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha