IQNA

Hamas Da Sauran Falastinawa Sun Yi Allawadai Da Ziyarar Firayi Ministan Isra'ila A UAE

21:35 - December 14, 2021
Lambar Labari: 3486684
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da ziyarar da firayi ministan Isra'ila ya kai kasar Hadaddiyar daular larabawa.

Isma'ila Ridwan daya daga cikin jagororin Hamas ya bayyana cewa, kugiyar tana yin Allah wadai da kakkausar murya da ziyarar da firayi ministan Isra'ila ya kai kasar Hadaddiyar daular larabawa.

Ya ci gaba da cewa wannan babban abin kunya ne ga sarakunan larabawa, ta yadda firayi ministan Isra'ila da ke kisan 'yan uwansu larabawa da musulmi a Falastinu, sarakunan larabawa suna tarbarsa da jar darduma a cikin kasashensu.

Ita ma a nata bangaren kungiyar Jihadul Islami ta bayyana ziyarar da firayi ministan gwamatin yahudawan Isra'ila ya kai yau a kasar Hadaddiyar daular Larabawa da cewa abin Allawadai ne ga duk wasu masu lamiri a cikin larabawa da musulmi.

Bayanin ya ce, yadda mahukuntan kasar kasar Hadaddiyar daular Larabawa suka fito suka yi wa Firayi ministan Isra'ila tarbe da lalae marhabin a cikin kasarsu, hakan yana nuni da amincewa da abin da Isra'ila take tafkawa na kisan kiyashi a kan al'ummar Falastinu, tare ad halasta mata a hakan a hukuamnce.

Jakadan Isra'ila a Hadaddiyar Daular Larabawa ya bayyana cewa, firaministan Isra'ila Naftali Bennett, zai tattauna batun Iran da kuma batutuwan da suka shafi Isra’ila da UAE, a wata ganawarsa da yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, Mohammed bin Zayed, a jiya Litinin.

4020880

 

 

 

 

 

captcha