IQNA

Shugaban Kasar Aljeriya Ya Jaddada Wajabcin Dawowar Syria Cikin Kungiyar Kasashen Larabawa

19:06 - December 16, 2021
Lambar Labari: 3486692
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Aljeriya Abdel Majid Taboun ya jaddada bukatar komawar kasar Syria a cikin kungiyar kasashen Larabawa, yana mai  cewa babu wata kasa da ke da hakkin tsoma baki cikin harkokin wata kasa.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ya yi da takwaransa na Tunisiya, Shugaban kasar Aljeriya Abdel Majid Taboun, ya jaddada wajabcin komawar Syria cikin kungiyar kasashen  Larabawa, inda ya ce sake hadewar kasashen Larabawa na bukatar Syria ta koma cikin kungiyar kasashen Larabawa, domin a cewarsa babu wani babban bambanci tsakanin kasashen Larabawa.

Shugaban na Aljeriya ya kuma bayyana fatansa na cewa taron kungiyar kasashen Larabawa da za a yi a watan Maris zai dawo da daidaito a tsakaninsu da fahimtar juna.

Abdel Majid Taboun wanda ya ziyarci kasar Tunisia inda ya gana da shugaban kasar Qais Saeed, ya ce ya gamsu da shawarwarin shugaban kasar Tunusiya, kan yadda za a warware rikicin Libiya cikin lumana, da kuma cewa sojojin haya da sojojin kasashen waje dole ne su fice daga kasar ta Libya.

Tun a watan Nuwamban shekara ta 2011 ne aka dakatar da kasar Siriya a matsayin ta kungiyar kasashen Larabawa, sakamakon matsin lamba na wasu kasashen da suka mamaye kungiyar, kuma suke shimfida siyasarsu a kanta yadda suka ga dama.

4021259

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha