IQNA

Jagoran Juyi A Iran Ya Yi Bayani Kan Cikar Shekaru Biyu Da Shahadar Qasem Sulaini

22:14 - January 01, 2022
Lambar Labari: 3486766
Tehran (IQNA) jagoran juyi a Iran ya yi bayani kan cikar shekaru biyu da shahadar Kasim Sulaimani.

Jarogan juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Ali Khamine’i ya ce shahid Kasim Sulaimani ya zama abin koyi ga matasa a yankin gabas ta tsakiya ko Asiya ta kudu.
 
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Imam Khami’na’ii yana fadar haka a safiyar yau Asabar a lokacin da yake ganawa da iyalan shahidin a gidansa.
 
Ya kuma kara da cewa abubuwan biyu ne suke maida shahid sulaimani abinda ya zama, na farki yin abu don neman yardar Allah da kuma riko da gaskiya cikin al-amuransa.
 
Imam Khamina’i ya kara da cewa da alamun mutanen kasar Iran sun fahinci wannan a wajen shahid sulaimani, shi ya sa suka kwansu da kwarkwatansu wajen jana’izarsa. Daga karshe Imam Khamina’ii ya kammala da cewa shahadar Shahid Kasim Sulaimani wani babban al-amanari ne kasar Iran da kuma duniya gaba daya.
 
Aranar 3 ga watan Jenerun shekara 2020 ne shugaban kasar Amurka na lokacin Dunal Trump ya ce shi ya bada umurni a kashe Janar Shahid Kasim Sulaimani bayan saukarsa a tashar jiragen sama na Bandaga a cikin kasar Iraki.
 
 

4025113

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: nakalto ، abubuwa ، ganawa ، shahid Qasim Sulaimani ، riko
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha