IQNA

Shugaban Iraki Ya Ce: Qassem Sulaimani Ya Kai Wa Iraki Dauki Cikin Gaggawa A Lokacin Da Take Bukatarsa

18:32 - January 05, 2022
Lambar Labari: 3486781
Tehran (IQNA) shugaban kasar Iran Barham Sale ya bayyana cewa Qassem Sulaimani bai wata-wata ba wajen kai wa al'ummar Iraki dauki a lokacin da suke matukar bukatar taimakonsa.
Shugaban kasar Iraki Barham Saleh ya bayyana cewa Janar Kasim Sulaimani na kasar Iran ya garzaya wajen cuton mutanen kasar Iraki daga mamayar kungiyar ‘yan ta’adda na Daesh a dai dai lokacinda kasar bata da mafita sai daga wajensa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Saleh yana fadar haka a jawabin da ya gabatar a taron tunawa da shahdar Sulaimani wanda dakarun Hashdushaabi na kasar Iraki suka shirya.
 
Shugaban ya kara da cewa, madallah da fatar Ayatullahi sayyid Sistani wanda ya bada fatawar jihadi kan kungiyar Daesh, fatawarda ta kai ga kafa dakarun Hashdu a shekara ta 2014 wacce tare da taimakon Janar Sulaimani da abokan aikinsa suke kwato mkasar Iraki daga hannun Daesh bayan shekaru 3 na fafatawa da Ita.
 
Amma saboda wannan gagarumin aikin da ya yi Amurka ta yi fushi da sannan ta kashe shi a dai dai lokacinda yake bako ga gwamnatin kasar Iraki. Shahid Kasim ya yi shahada tare da Abu Almuhandis abokin aikinsa a wannan aikin, sannan tare da wadanda suke rakiyarsu.
Abubuwan Da Ya Shafa: taron tunawa ، fatawar jihadi ، kasar Iraki ، tunawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha