IQNA

'Yan ta'addar Ansar al-Muslim sun shiga kungiyar Al-Qaeda a arewa maso yammacin Afirka

20:10 - January 05, 2022
Lambar Labari: 3486784
Tehran (IQNA) Kungiyar 'yan ta'adda ta Ansar al-Muslimin a bilad Sudan da ke yammacin Afirka ta sanar da cewa ta shiga cikin kungiyar al-Qaeda a yankin Magrib.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, Kungiyar 'yan ta'adda ta Jama'at Ansar al-Muslimin ta 'yan salafiyya da ke yammacin Afirka, ta sanar da cewa ta shiga kungiyar Al-Qaeda a yankin Magrib.

Kungiyar ta'addancin da akr ayyukanta a  yammacin Afirka ta fitar da wata sanarwa inda ta yi mubayi'a ga kungiyar Al-Qaeda, inda ta ce za ta fadada ayyukanta fiye da iyakokin kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, kuma yankinta ya kama daga arewacin Nijar zuwa gabar yammacin kogin Jordan. 
 
A cewar rahoton, idan har bayanan da ake samu suka tabbata, to akwai yiwuwar mayakan kungiyar 'yan ta'addan da ke yammacin Afirka za ta kafa sansanoni na hadin gwiwa a yankin nan da watanni masu zuwa.
 
Wannan lamari dai ya biyo bayan kalaman da Abu Ubaydah Yusuf al-Nabi shugaban kungiyar al-Qaeda reshen Magrib ne da ya yi a baya-bayan nan, inda ya ce a duk lokacin da muka samu dama, za mu ci gaba da ayyukanmu na jihadi.
 
https://iqna.ir/fa/news/4026373
captcha