
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa an gudanar da juyayin shahadar ne a husainiyyar, inda jagoran da wadanda suke karatun juyayin ne kawai suke shiga wurin, don kiyaye dokokin hada yaduwar cutar corona da ake fama da ita a kasar.
Fatima (s) ita ce diyar manzon Allah (s) sannan matar Imam Ali (a) sannan mahaifiya ga Imam Hassan da Husain (a).
Shahadarta ta kasance ne a cikin watan Jumada Thani watanni kadan bayan wafatin mahaifinta manzon Allah (s).
https://iqna.ir/fa/news/4026975