IQNA

An yanke wa hambararriyar shugabar Myanmar hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari

22:32 - January 10, 2022
Lambar Labari: 3486804
Tehran (IQNA) Wata kotu a Myanmar ta yanke wa tsohuwar shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari a yau Litinin.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, A cewar wata majiya da ke da masaniya kan lamarin Aung San Suu Kyi, an yanke mata hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari kan daya daga cikin tuhume-tuhume da ake yi mata.

Majiyar ta ce akwai wasu tuhume-tuhume da ake yi wa tsohuwar shugabar Myanmar, wanda zai kai ga daurin shekaru a gidan yari.

A cewar majiyar, Sochi, wacce ke tsare tun bayan juyin mulkin ranar 1 ga watan Fabrairun 2021, an same ta da laifin shigo da na’urori marasa lasisi.

Sochi dai ta musanta zargin, tana mai cewa ba su da tushe balle makama, kuma akwai siyasa cikin batun, ta jaddada cewa sojojin Myanmar ne suka yi wannan zargin domin kawo karshen mulkin dimukradiyya.

A watan Disamba da ya gabata, an bayar da rahoton cewa, an yanke wa tsohowar shugabar Myanmar hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari saboda ta karya dokar hana fita da aka yi saboda Corona, hukuncin da majalisar sojin kasar ta yanke daga baya zuwa shekaru biyu.

 

4027558

 

 

captcha